6 Ya rasa abin da zai faɗa ne, don sun tsorata da gaske.
6 (Bai san abin da zai faɗa ba ne, gama sun tsorata ƙwarai.)
Da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa kamar na mutu. Amma ya ɗora mini hannunsa na dama, ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne na Farko. Ni ne na Ƙarshe,
Sai Bitrus ya sa baki, ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, ya kyautu da muke nan wurin, mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.”
Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena. Ku saurare shi.”
Mutanen nan na rabuwa da shi ke nan, sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Maigida, ya kyautu da muke nan wurin. Mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.” Bai ma san abin da yake faɗa ba.