Jama'ar Sihiyona cike da zunubi suke, suna ta rawar jiki don tsoro. Suka ce, “Hukuncin Allah kamar wuta ce mai ci har abada. Akwai wani daga cikinmu da zai iya tsira daga irin wannan wuta?”
Sa'ad da suke tafiya, za su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa. Tsutsotsin da suke cinsu ba za su taɓa mutuwa ba, wutar da take ƙona su kuma ba za ta taɓa mutuwa ba. Dukan mutane za su ji ƙyamarsu.”
Ƙwaryar shiƙarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai sarai, ya taro alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun, sai ya ƙone a wutar marar kasuwa.”
zai ci karo da azabar Allah tsantsa ta tsananin fushinsa, za a kuwa azabta shi da wuta, da duwatsun wuta, a gaban mala'iku tsarkaka, da kuma Ɗan Ragon.
Shi kuwa Ibilis mayaudarinsu, sai da aka jefa shi a tafkin wuta da ƙibiritu, a inda dabbar nan da annabin nan na ƙarya suke, za a kuma gwada musu azaba dare da rana har abada abadin.
Amma matsorata, da marasa riƙon amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibiritu, wanda yake shi ne mutuwa ta biyu.”