Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Markus 9:3 - Littafi Mai Tsarki

3 tufafinsa suka yi fari fat suna sheƙi, yadda ba mai wankin da zai iya yinsu haka a duniya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Tufafinsa suka zama fari suna ƙyalli, fiye da yadda wani a duniya zai iya yi su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Markus 9:3
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kamanninsa suna haske kamar walƙiya, tufafinsa kuma farare fat kamar dusar ƙanƙara.


“Ina dubawa sai na ga an ajiye gadajen sarauta, Sai wani wanda yake Tun Fil Azal ya zauna kursiyinsa. Rigarsa fara fat kamar dusar ƙanƙara, Gashin kansa kamar ulu ne tsantsa, Kursiyinsa harshen wuta ne, Ƙafafun kursiyin masu kamar karusa, wuta ne.


Sai na ce masa, “Ya shugaba, ai, ka sani.” Sai ya ce mini, “Su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala, sun wanke rigunansu, suka mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan.


Bayan wannan na duba, ga wani ƙasaitaccen taro, wanda ya fi gaban ƙirge, daga kowace al'umma, da kabila, da jama'a, da harshe, suna a tsaitsaye a gaban kursiyin, a gaban Ɗan Ragon kuma, a saye da fararen riguna, da gazarin dabino a hannunsu,


Sai Karniliyas ya ce, “Yau kwana uku ke nan, wajen war haka, ina addu'ar ƙarfe uku na yamma a gidana, sai ga wani mutum tsaye a gabana, yana saye da tufafi masu ɗaukar ido,


Ubangiji ya ce, “Yanzu fa, bari mu daidaita al'amarinmu. Duk kun yi ja wur da zunubi, amma zan wanke ku, ku yi fari fat kamar auduga. Zai yiwu zunubinku ya sa ku zama ja wur, amma za ku yi fari fat kamar farin ulu.


Sa'ad da Allah Mai Iko Dukka Ya warwatsar da sarakuna a dutsen Zalmon, Sai ya sa dusar ƙanƙara ta sauka a wurin.


Ka kawar da zunubina, zan kuwa tsarkaka, Ka wanke ni, zan kuwa fi auduga fari.


ku ci naman sarakuna, da naman sarakunan yaƙi, da naman ƙarfafa, da naman dawakai, da na mahayansu, da naman kowa da kowa, wato, na ɗa da na bawa, na yaro da na babba.”


Sai Iliya da Musa sun bayyana a gare su, suna magana da Yesu.


Yana yin addu'a, sai kama tasa ta sāke, tufafinsa kuma suka yi fari fat, har suna ɗaukar ido.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ