Markus 9:12 - Littafi Mai Tsarki12 Sai ya ce musu, “Lalle ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwa. Yaya kuwa yake a rubuce a kan Ɗan Mutum, cewa zai sha wuya iri iri, a kuma wulaƙanta shi? အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya ne, Iliya zai zo da fari, yă kuma mayar da dukan abubuwa. Don me kuma aka rubuta cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahala sosai, kuma a ƙi shi? အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.