26 Sai Yesu ya sallame shi ya koma gida, ya ce, “Ko ƙauyen ma kada ka shiga.”
26 Yesu ya sallame shi gida ya ce, “Kada ka shiga cikin ƙauyen.”
Sai Yesu ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”
Ya kama hannun makahon, ya kai shi bayan gari. Da ya tofa yau a idanunsa, ya ɗora masa hannu, sai ya tambaye shi cewa, “Kana iya ganin wani abu?”
Yesu ya kwaɓe su kada su faɗa wa kowa, amma ƙara yawan kwaɓonsu ƙara yawan yaɗa labarin.
Sai ya kwaɓe su matuƙa kada kowa ya ji wannan labari. Ya kuma yi umarni a ba ta abinci.
Sai ya kwaɓe su, kada su bayyana shi.
Sai idanunsu suka buɗe. Amma Yesu ya kwaɓe su ƙwarai, ya ce, “Kada fa kowa ya ji labarin.”
Sai ya sāke ɗora hannu a idanunsa. Makahon kuwa ya zura ido ƙwar, ya warke, ya ga kome garau.