Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Markus 8:2 - Littafi Mai Tsarki

2 “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna, ba su da wani abinci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 “Ina jin tausayin mutanen nan, kwanansu uku ke nan tare da ni, kuma ba su da abin da za su ci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Markus 8:2
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma da ya ga taro masu yawa sai ya ji tausayinsu, domin suna shan wahala, suna nan a warwatse kamar tumaki da ba makiyayi.


Zai sāke jin juyayinmu, Ya tattake muguntarmu a ƙarƙashin ƙafafunsa. Za ka jefar da zunubanmu a cikin zurfin teku.


Dukan masu rai suna sa zuciya gare shi, Yana ba su abinci a lokacin da suke bukata,


Kamar yadda uba yake yi wa 'ya'yansa alheri, Haka nan kuwa Ubangiji yake yi wa masu tsoronsa alheri.


Yă kuma zamana wanda zai iya tafiyar da jahilai da sangartattu a cikin salihanci, tun da yake rarrauna ne shi ta ko'ina.


Gama Babban Firist da muke da shi ba marar juyayin kasawarmu ba ne, a'a, shi ne wanda aka jarabce shi ta kowace hanya da aka jarabce mu, amma bai yi zunubi ba.


Sai ya tashi, ya taho wurin ubansa. Amma tun yana daga nesa, sai ubansa ya hango shi, tausayi ya kama shi, ya yiwo gudu, ya rungume shi, ya yi ta sumbatarsa.


Da Ubangiji ya gan ta, ya ji tausayinta, ya kuma ce mata, “Daina kuka.”


Ya kuwa sha jefa shi a wuta da ruwa, don ya hallaka shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.”


Da saukar Yesu sai ya ga taro mai yawa, ya kuma ji tausayinsu, domin kamar tumaki suke ba makiyayi. Ya fara koya musu abubuwa da yawa.


Amma Yesu bai yardar masa ba, ya ce masa, “Tafi gida wurin 'yan'uwanka, ka faɗa musu irin manyan abubuwan da Ubangiji ya yi maka, da kuma yadda ya ji tausayinka.”


Da tausayi ya kama Yesu, sai ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce masa, “Na yarda, ka tsarkaka.”


Domin tausayi, sai Yesu ya taɓa idanunsu, nan take suka gani, suka bi shi.


Da ya fita daga jirgin ya ga babban taron mutane. Sai ya ji tausayinsu, ya kuma warkar da marasa lafiya a cikinsu.


Ubangiji mai ƙauna ne, mai jinƙai, mai jinkirin fushi, Cike da madawwamiyar ƙauna.


Saboda haka, lalle ne yă zama kamar 'yan'uwansa ta kowane hali, domin yă zama Babban Firist, mai jinƙai, mai aminci kuma na al'amarin Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama'a.


Sai suka tafi cikin jirgi wurin da ba kowa, su kaɗai.


In kuwa na sallame su su tafi gida da yunwa haka, ai, za su kasa a hanya, ga shi kuwa, waɗansunsu sun fito nesa.”


Da ya duba, sai ga waina da zafinta a bisa duwatsu, da butar ruwa a waje ɗaya. Ya ci, ya sha, ya koma kwantawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ