Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane sun ce suna mini sujada, amma kalmominsu ba su da ma'ana, zukatansu kuma suna wani wuri dabam. Addininsu ba wani abu ba ne, sai dai dokoki ne da ka'idodin mutane da suka haddace.
Ina yi wa duk mai jin maganar annabcin littafin nan kashedi, in wani ya yi wani ƙari a kanta, Allah zai ƙara masa bala'in da aka rubuta a littafin nan.
Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Ubangiji. Ina amfani a kiyaye abin da ya ce, ko mu yi ƙoƙarin nuna cewa zuciyarmu ta ɓāci saboda ayyukan da muka yi wa Ubangiji Mai Runduna.
Don haka, ya 'yan'uwana, ƙaunatattu, ku tsaya a kafe, kullum kuna himmantuwa ga aikin Ubangiji, domin kuwa kun san famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.