30 Sai ta koma gida ta iske yarinyar a kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.
30 Ta tafi gida, ta tarar da diyarta kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.
Duk mai aikata zunubi, na Iblis ne, don tun farko Iblis mai aikata zunubi ne. Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne domin yă rushe aikin Iblis.
Sai ya ce mata, “Saboda wannan magana taki, koma gida, aljanin, ai, ya rabu da 'yarki.”
Sai ya komo daga wajen Taya, ya bi ta Sidon ya je Tekun Galili ta Dikafolis.