9 amma su sa takalmi, kada kuma su haɗa taguwa biyu.
9 Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa.
Mala'ikan ya ce masa, “Yi ɗamara, ka sa takalminka.” Sai ya yi. Sai ya ce masa, “Yafa mayafinka, ka biyo ni.”
shirin kai bisharar salama ya zama kamar takalmi a ƙafafunku.
“Ni dai, da ruwa nake muku baftisma, shaidar tubarku, amma mai zuwa bayana, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.
kada kuma ku ɗauki burgami a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma'aikaci ya cancanci hakkinsa.
Ya umarce su kada su ɗauki guzuri don tafiyar, ko gurasa, ko burgami, ko kuɗi ma a ɗamararsu, sai dai sanda kawai,
Ya ce musu, “Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi.