Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Markus 6:41 - Littafi Mai Tsarki

41 Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a, duk kuma ya raba musu kifin nan biyu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

41 Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Markus 6:41
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan ya umarci taron su zazzauna a ɗanyar ciyawa. Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiransa, almajiran kuma suna bai wa jama'a.


Ya ɗaga kai sama ya yi ajiyar zuciya, sai ya ce masa, “Iffata!” wato “Buɗu!”


Sa'ad da yake cin abinci tare da su, sai ya ɗauki gurasa, ya yi wa Allah godiya, ya gutsura, ya ba su.


Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyu, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura su, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a.


Da shigarku garin, za ku same shi kafin ya tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu, gama jama'a ba za su ci ba, sai ya je ya sa albarka a sadakar, sa'an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura yanzu, za ku same shi nan da nan.”


To, duk abin da kuke yi, ko ci, ko sha, ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.


Da Yesu ya faɗi haka, sai ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka domin Ɗan ya ɗaukaka ka,


Sai suka kawar da dutsen. Yesu kuwa ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, na gode maka da ka saurare ni.


Suna cikin cin abinci, sai ya ɗauki gurasa, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Ungo, wannan jikina ne.”


Kome kuke yi, a game da magana ko aikatawa, ku yi duka da sunan Ubangiji Yesu, kuna gode wa Allah Uba ta wurinsa.


Mai kiyaye wata rana musamman, yana kiyaye ta ne saboda Ubangiji. Mai cin nan kuma, yana ci ne saboda Ubangiji, da yake yana gode wa Allah. Marar cin nan kuma yana ƙin ci ne saboda Ubangiji, shi ma kuwa yana gode wa Allah.


Akwai kuwa waɗansu ƙananan jirage daga Tibariya da suka iso kusa da wurin nan da taron suka ci gurasa bayan Ubangiji ya yi godiya.


Yesu ya ɗauki gurasar, bayan ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya rarraba wa waɗanda suke zazzaune. Haka kuma ya yi da kifin, gwargwadon abin da ya ishe su.


Suna cikin cin abinci, sai Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba almajiran, ya ce, “Ungo, ku ci. Wannan jikina ne.”


Da ya ɗauki gurasa bakwai ɗin da kifayen nan, ya yi godiya ga Allah, sai ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiran, almajiran kuma na, bai wa jama'a.


Sa'ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda kyakkyawar ƙasa mai albarka da ya ba ku.”


Da ya faɗi haka, ya ɗauki curin gurasa, ya yi godiya ga Allah a gabansu duka, sa'an nan ya gutsuttsura ya fara ci.


Haka suka zauna jeri jeri, waɗansu ɗari ɗari, waɗansu hamsin hamsin.


Da na gutsuttsura wa mutum dubu biyar gurasan nan biyar, kwando nawa kuka ɗauka cike da gutsattsarin?” Suka ce masa, “Sha biyu.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ