Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Markus 6:34 - Littafi Mai Tsarki

34 Da saukar Yesu sai ya ga taro mai yawa, ya kuma ji tausayinsu, domin kamar tumaki suke ba makiyayi. Ya fara koya musu abubuwa da yawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 Da Yesu ya sauka, ya ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu, gama kamar tumaki suke waɗanda ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Markus 6:34
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma da ya ga taro masu yawa sai ya ji tausayinsu, domin suna shan wahala, suna nan a warwatse kamar tumaki da ba makiyayi.


mutumin da zai shugabance su cikin yaƙi, don kada taron jama'ar Ubangiji su zama kamar tumakin da ba su da makiyaya.”


Ganin haka sai taro masu yawa suka bi shi. Ya kuwa yi musu maraba, ya yi musu maganar Mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkewa.


Gama maganar shirme kan gida yake yi, Masu dūba suna ganin wahayin ƙarya, Masu mafarkai suna faɗar ƙarya, Ta'aziyyarsu ta banza ce. Domin haka mutane suna ta yawo kamar tumaki, Suna shan wahala saboda rashin makiyayi.


“Mutanena sun zama kamar ɓatattun tumaki, Waɗanda makiyayansu suka bauɗar da su, Suka ɓata a cikin tsaunuka, Suna kai da kawowa daga wannan dutse zuwa wancan. Sun manta da shingensu.


Mikaiya kuwa ya ce, “Ina ganin dukan Isra'ilawa a warwatse bisa tsaunuka, kamar tumakin da ba su da makiyayi. Ubangiji kuma ya ce, ‘Waɗannan ba su da makiyayi, bari dukansu, kowa ya koma gidansa da salama.’ ”


Mikaiya ya ce, “Na ga mutanen Isra'ila duka a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, Ubangiji kuwa ya ce, ‘Waɗannan ba su da shugaba, bari kowa ya koma gidansa lafiya.’ ”


Gama Babban Firist da muke da shi ba marar juyayin kasawarmu ba ne, a'a, shi ne wanda aka jarabce shi ta kowace hanya da aka jarabce mu, amma bai yi zunubi ba.


Da ya fita daga jirgin ya ga babban taron mutane. Sai ya ji tausayinsu, ya kuma warkar da marasa lafiya a cikinsu.


Saboda haka, lalle ne yă zama kamar 'yan'uwansa ta kowane hali, domin yă zama Babban Firist, mai jinƙai, mai aminci kuma na al'amarin Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama'a.


Yesu ya kira almajiransa, ya ce, “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna ba su da wani abinci. Ba na kuwa so in sallame su da yunwa haka, kada su kasa a hanya.”


“Baƙin da yake zaune a Babila za su gudu zuwa ƙasashensu, suna a warwatse kamar bareyin da suke tsere wa maharbansu, kamar tumakin da ba su da makiyayi.


Sai suka warwatsu saboda rashin makiyayin kirki, suka zama abincin namomin jeji.


Ashe, mutane da yawa sun ga tafiyarsu, sun kuwa shaida su, suka fa dunguma ta tudu daga garuruwa duka, suka riga su zuwa.


Kusan faɗuwar rana sai almajiransa suka zo gare shi, suka ce masa, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuwa, rana ta kusa fāɗuwa.


A lokacin nan da wani taro mai yawan gaske ya sāke haɗuwa, ba su kuwa da abinci, sai ya kira almajiransa, ya ce musu,


“Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna, ba su da wani abinci.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ