Markus 6:3 - Littafi Mai Tsarki3 Shin, wannan ba shi ne masassaƙin nan ba, ɗan Maryamu, ɗan'uwan su Yakubu, da Yusufu, da Yahuza, da kuma Saminu? 'Yan'uwansa mata kuma ba ga su tare da mu ba?” Suka yi tuntuɓe sabili da shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗan’uwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ’yan’uwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.