Sai Bitrus ya ce musu, “Sai ku tuba, a yi wa ko wannenku baftisma, a kan kun yarda da sunan Yesu Almasihu, domin a gafarta zunubanku, za ku kuwa sami baiwar Ruhu Mai Tsarki,
A Ranar Shari'a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan su kā da su. Don sun tuba saboda wa'azin Yunusa. To, ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan.”
“Domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta ku, ku mutanen Isra'ila, kowa gwargwadon ayyukansa. Ku tuba, ku bar laifofinku domin kada su zama muku dalilin halaka.
Da fari, na yi wa mutanen Dimashƙu wa'azi, sa'an nan na yi a Urushalima da dukan kewayen ƙasar Yahudiya, sa'an nan kuma na yi wa al'ummai, cewa su tuba su juyo ga Allah, su kuma yi aikin da zai nuna tubarsu.
Ina dai gaya muku, haka kuma, za a yi farin ciki a Sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan adalai tasa'in da tara waɗanda ba su bukatar tuba.”
Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba.’ Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi.”