Aljannu kuma suka fita daga mutane da yawa, suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya tsawata musu, ya hana su magana, don sun sani shi ne Almasihu.
Ku faɗa wa Allah cewa, “Al'amuran da kake aikatawa Suna da banmamaki ƙwarai! Ikonka yana da girma ƙwarai, Har maƙiyanka sukan durƙusa a gabanka don tsoro.