Har ma ya kai ga suna fito da marasa lafiya tafarku, suna shimfiɗa su a kan gadaje da tabarmi, don in Bitrus ya zo wucewa, ko da inuwa tasa ma ta bi ta kan waɗansunsu.
Duk inda ya shiga kuma, birni ko ƙauye ko karkara, sukan kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa, su roƙe shi su taɓa ko ma da gezar mayafinsa ma. Iyakar waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.
Wata rana ana binne gawa, sai aka ga mahara, aka jefar da gawar a cikin kabarin Elisha. Da gawar ta taɓi ƙasusuwan Elisha, sai ya farko ya tashi ya miƙe tsaye.