25 Sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini,
25 A can kuwa akwai wata mace, wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini.
sai ga wata mace wadda inna ta shanye tun shekara goma sha takwas, duk ta tanƙware, ko kaɗan ba ta iya miƙewa.
Mutumin nan da aka yi wa mu'ujizar nan ta warkarwa kuwa ya ba shekara arba'in baya.
Sai suka tafi tare. Babban taro kuwa na biye da shi, suna matsa tasa.
ta kuma sha wahala da gaske a hannun masu magani da yawa, har ta ɓad da duk abin da take da shi, amma duk a banza, sai ma gaba-gaba cutar take yi.