Ku saurara, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?
“Yanzu, ya Isra'ilawa, sai ku kiyaye dokoki da farillai da nake koya muku don ku rayu, ku shiga ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku suke ba ku.
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin cin 'ya'yan itacen rai, wanda yake a cikin Firdausin Allah.’ ”
Amma Bitrus ya miƙe tare da sha ɗayan nan, ya ɗaga murya ya yi musu jawabi, ya ce, “Ya ku 'yan'uwana Yahudawa da dukan mazaunan Urushalima, ku kula da wannan, ku kuma saurari maganata.
Ka shuka iri da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka.