Sai Yesu ya tashi daga nan, ya tafi ƙasar Yahudiya, da kuma hayin Kogin Urdun. Taro kuma ya sāke haɗuwa wurinsa, ya kuma sāke koya musu kamar yadda ya saba.
Sai Yesu ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabin, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.