25 Haka in gida ya rabu a kan gāba, wannan gida ba zai ɗore ba.
25 In gida yana gāba da kansa, wannan gida ba zai tsaya ba.
A duk inda kishi da sonkai suke, a nan hargitsi da kowane irin mugun aiki ma suke.
Amma in kuna cin naman juna, ku mai da hankali fa, hanyar hallaka juna ke nan.
Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma, Ga jama'ar Allah su zauna tare kamar 'yan'uwa!
Amma sa'ad da 'yan'uwansa suka gane mahaifinsu yana ƙaunarsa fiye da dukansu, suka ƙi jininsa, ba su iya maganar alheri da shi.
Ai, in mulki ya rabu a kan gāba, wannan mulki ba zai ɗore ba.
Shaiɗan kuma in ya tayar wa kansa, ya rabu, ba zai ɗore ba, ƙarewa tasa ce ta zo.