Sa'an nan kuma na karya sandana na biyun mai suna “Haɗa Kai,” wato alama ke nan da ta nuna na kawar da 'yan'uwancin da yake tsakanin Yahuza da Isra'ila.
Zan maishe su al'umma guda a ƙasar Isra'ila. Sarki ɗaya zai sarauce su duka, ba za su ƙara zama al'umma biyu ba, ba kuwa za su ƙara zama masarauta biyu ba.
Dawuda kuma ya ce wa Abishai, “Sheba ɗan Bikri fa, zai ba mu wuya fiye da Absalom, sai ka ɗauki mutanena, ka bi sawunsa, don kada ya ci garuruwa masu garu har ya tsere mana.”
Da can akwai wani mutumin banza, ana ce da shi Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Biliyaminu. Shi kuwa ya busa ƙaho, ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu kuwa da gado wurin ɗan Yesse. Ya Isra'ilawa, kowa ya gudu zuwa alfarwarsa.”
domin dukansu su zama ɗaya, kamar yadda kai, ya Uba, kake cikina, ni kuma nake cikinka, haka su ma su kasance cikinmu, domin duniya ta gaskata, cewa kai ne ka aiko ni.