13 Ya hau dutse, ya kira waɗanda yake so, suka je wurinsa.
13 Yesu ya hau gefen wani dutse, ya kira waɗanda yake so, suka kuma zo wurinsa.
Sai ya tara goma sha biyun nan ya ba su iko da izini kan dukan aljannu, su kuma warkar da cuce-cuce,
Sai ya kira goma sha biyun nan, ya fara aikensu biyu-biyu, ya kuma ba su iko a kan baƙaƙen aljannu.
Da Yesu ya ga taro masu yawa sai ya hau dutse. Da ya zauna, almajiransa kuma suka zo gunsa.
Ya zaɓi mutum goma sha biyu su zauna tare da shi, ya riƙa aikensu suna wa'azi.
Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa.