Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Markus 2:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Yadda ya shiga masujadar Allah a zamanin Abiyata babban firist, ya ci keɓaɓɓiyar gurasan nan, wadda bai halatta kowa ya ci ba, sai firistoci kaɗai, har ma ya ba abokan tafiyarsa?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Ya shiga gidan Allah a zamanin Abiyatar babban firist, ya ci keɓaɓɓen burodin nan, ya kuma ba wa abokan tafiyarsa abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Markus 2:26
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zadok ɗan Ahitub, da Ahimelek ɗan Abiyata, su ne firistoci. Seraiya shi ne magatakarda.


Shemaiya, ɗan Netanel marubuci, Balawe, ya rubuta su a gaban sarki da shugabanni, da Zadok firist, da Ahimelek ɗan Abiyata, da shugabannin gidajen kakannin firistoci, da Lawiyawa. Aka ɗauki gida guda daga gidajen kakannin Ele'azara, aka kuma ɗauki ɗaya daga gidajen kakannin Itamar.


Sa'an nan Dawuda ya tafi wurin Ahimelek, firist, a Nob. Ahimelek kuwa ya fita da rawar jiki domin ya tarye Dawuda, ya ce masa, “Me ya sa kake kai kaɗai, ba wani tare da kai ba?”


Sai sarki Sulemanu ya amsa wa tsohuwarsa, ya ce, “Don me kika roƙar wa Adonija Abishag? Ki roƙar masa sarautar mana, gama shi wana ne, Abiyata, firist kuma, da Yowab ɗan Zeruya suna goyon bayansa.”


Ya gama baki da Yowab ɗan Zeruya, da Abiyata, firist. Su kuwa suka yarda su goyi bayansa, su taimake shi.


Shewa shi ne magatakarda. Zadok da Abiyata su ne firistoci.


Ga shi, Zadok da Abiyata, firistoci, suna tare da kai. Duk abin da ka ji daga gidan sabon sarki, sai ka faɗa wa Zadok da Abiyata, firistoci.


Zadok da Abiyata kuwa suka ɗauki akwatin alkawari suka koma Urushalima, suka zauna a can.


Sai ga Abiyata ya zo, sai kuma ga Zadok ya zo tare da dukan Lawiyawa, ɗauke da akwatin alkawarin Allah. Suka ajiye akwatin har dukan mutane suka gama fita daga birnin.


Dawuda kuwa ya sani Saul yana shirya hanyar kashe shi, sai ya ce wa Abiyata, firist, “Kawo falmaran a nan.”


Lokacin da Abiyata ɗan Ahimelek, ya gudu zuwa wurin Dawuda a Kaila, ya zo da falmaran a hannunsa.


Yadda ya shiga Ɗakin Allah ya ci keɓaɓɓiyar gurasar nan, wadda bai halatta ya ci ba, ko abokan tafiyarsa ma su ci ba, sai dai firistoci kaɗai?


Sai ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba, sa'ad da ya matsu da yunwa, shi da abokan tafiyarsa?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ