Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Markus 2:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Ai, lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa’an nan ne fa za su yi azumi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Markus 2:20
29 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya kuma ce wa almajiran, “Lokaci na zuwa da za ku yi begen ganin rana ɗaya daga cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba.


Sai kuma ɗaya daga cikin mala'ikun nan bakwai, masu tasoshin nan bakwai, cike da bala'i bakwai na ƙarshe, ya zo ya yi mini magana, ya ce, “Zo in nuna maka amarya, matar Ɗan Ragon.”


Mu yi ta murna da farin ciki matuƙa, Mu kuma ɗaukaka shi, Domin bikin Ɗan Ragon nan ya zo, Amaryarsa kuma ta kintsa.


Na sha fama, na sha wuya, na sha rashin barci, na sha yunwa da ƙishirwa, sau da yawa na rasa abinci, na sha sanyi da huntanci.


Ina kishi a kanku saboda Allah. Gama na bashe ku ga Almasihu, domin in miƙa ku kamar amarya tsattsarka ga makaɗaicin mijinta.


Kada ɗayanku yă ƙaurace wa ɗaya, sai ko da yardar juna zuwa wani ɗan lokaci kaza, don ku himmantu ga addu'a, sa'an nan ku sāke haɗuwa, kada Shaiɗan yă zuga ku ta wajen rashin kamewa.


Bayan kuma sun zaɓar musu dattawa a kowace Ikkilisiya, game da addu'a da azumi, suka danƙa su ga Ubangiji, wanda dā ma suka gaskata da shi.


wanda lalle ne ya zauna a Sama, har kafin lokacin nan na sabunta dukkan abubuwa da Allah ya faɗa tun zamanin dā ta bakin annabawansa tsarkaka.


Da ya faɗi haka, suna cikin dubawa, sai aka ɗauke shi Sama, wani gajimare ya tafi da shi, ba su ƙara ganinsa ba.


Amma yanzu ina zuwa wurinka. Ina faɗar wannan magana tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu.


Yanzu kuma ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai tsarki, ka kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni, su zama ɗaya kamar yadda muke.


Daga wurin Uban ne na fito, na shigo duniya, har wa yau kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.”


Duk da haka ina gaya muku gaskiya, zai fiye muku in tafi, domin in ban tafi ba, Mai Taimakon nan ba zai zo gare ku ba. In kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku.


Ya ku 'ya'yana ƙanana, saura ɗan lokaci kaɗan ina tare da ku. Za ku neme ni, amma kamar yadda na faɗa wa Yahudawa cewa, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba,’ haka nake faɗa muku yanzu.


Mai amarya shi ne ango. Abokin ango kuwa da yake tsaye, yake kuma sauraron magana tasa, yakan yi farin ciki ƙwarai da jin muryar angon. Saboda haka farin cikin nan nawa ya cika.


Sai Yesu ya ce musu, “Duk za ku yi tuntuɓe sabili da ni a wannan dare domin a rubuce yake cewa, ‘Zan bugi makiyayi, tumakin garken kuwa za su fasu.’


“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Ubangiji zai ɗauke ki amaryarsa, Za ku yi murna tare, Kamar murnar amarya da ango.


Mahaliccinki zai zama kamar miji a gare ki, Sunansa Ubangiji Mai Runduna! Allah Mai Tsarki na Isra'ila mai fansarki ne, Shi ne mai mulkin dukan duniya!


Matan Sihiyona, ku fito ku ga sarki Sulemanu Ya sa kambin sarauta, Wanda uwarsa ta sa masa, a ranar aurensa, A ranarsa ta murna da farin ciki.


Saboda ke kyakkyawa ce sarki zai so ki, Shi ne maigidanki, sai ki yi masa biyayya.


da shan dūka, da shan ɗauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rasa barci, da kuma rasa abinci.


Ai, kullum kuna tare da gajiyayyu, amma ba kullum kuke tare da ni ba.”


Sai Yesu ya ce musu, “Abokan ango sa yi baƙin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.


Sai Yesu ya ce musu, “Ashe, abokan ango sa iya azumi tun ango na tare da su? Ai, muddin suna tare da angon, ba za su yi azumi ba.


Ba mai mahon tsohuwar tufa da sabon ƙyalle. In ma an yi, ai, sai sabon ƙyallen ya kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa.


Ai, lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ