8 Jama'a fa suka matso, suka fara roƙon Bilatus ya yi musu abin da ya saba yi.
8 Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yă yi musu abin da ya saba yi.
To, a lokacin idi kuwa mai mulki ya saba sakar wa jama'a kowane ɗaurarre guda da suka so.
Sai Yesu ya tashi daga nan, ya tafi ƙasar Yahudiya, da kuma hayin Kogin Urdun. Taro kuma ya sāke haɗuwa wurinsa, ya kuma sāke koya musu kamar yadda ya saba.
Akwai wani wai shi Barabbas da yake ɗaure, tare da waɗansu 'yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin tawayen.
Sai ya amsa musu, ya ce, “Wato kuna so ne in sakar muku Sarkin Yahudawa?”
Za ku turke dabbar har rana ta goma sha huɗu ga wata, wato sa'ad da dukan taron jama'ar Isra'ila za su yanka ragunansu da maraice.