Aka ƙware shi ba tausayi, Amma ya karɓa da tawali'u, Bai ko ce uffan ba. Kamar ɗan rago wanda ake shirin yankawa, Kamar tunkiya wadda ake shirin yi wa sausaya, Bai ko ce uffan ba.
Don a ganina, Allah ya bayyana mu, mu manzanni, koma bayan duka ne, kamar waɗanda mutuwa yake jewa a kansu, don mun zama abin nuni ga duniya, da mala'iku duk da mutane.
Ga ni tare da 'ya'yan da Ubangiji ya ba ni. Ubangiji Mai Runduna, wanda kursiyinsa a kan Dutsen Sihiyona yake, ya maishe mu rayayyen jawabi ga jama'ar Isra'ila.