Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Markus 15:34 - Littafi Mai Tsarki

34 Da ƙarfe ukun sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktāna?” wato “Ya Allahna, Ya Allahna, don me ka yashe ni?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Markus 15:34
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya Allahna, ya Allahna, Don me ka yashe ni? Na yi kuka mai tsanani, ina neman taimako, Amma har yanzu ba ka zo ba!


Wajen ƙarfe uku kuma sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktāni?” Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”


Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roƙe-roƙe, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsananin miƙa kansa.


Kada ka ɓoye mini fuskarka, ya Ubangiji! Kada ka yi fushi da ni, Kada kuwa ka kori bawanka. Kai ne kake taimakona, tun dā ma, Kada ka bar ni, kada ka yashe ni, Ya Allahna, Mai Cetona!


Suna cewa, “Ai, Allah ya rabu da shi, Gama ba wanda zai cece shi!”


Sa'ad da nake yin addu'a, sai mutumin nan Jibra'ilu, wanda na gani a wahayin da ya wuce, ya zo wurina a gaggauce wajen lokacin yin hadaya ta maraice.


“Sa'ad da jama'ata ta bukaci ruwa, Sa'ad da maƙogwaronsu ya bushe da ƙishi, Sa'an nan ni Ubangiji, zan amsa addu'arsu, Ni Allah na Isra'ila, ba zan taɓa yashe su ba.


Ga Allah wanda yake tsarona na ce, “Me ya sa ka manta da ni? Me ya sa nake ta shan wahala Saboda muguntar maƙiyana?”


Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma, ya ga wani mala'ikan Allah a fili cikin wahayi, ya shigo, ya ce masa, “Ya Karniliyas.”


Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ya Uba, na sa ruhuna a ikonka.” Da ya faɗi haka kuwa, sai ya cika.


To, wajen tsakar rana ne kuwa, sai duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma.


Don me ka manta da mu har abada? Don me ka yashe mu da daɗewa haka?


“Dukanku masu wucewa, ba wani abu ba ne a gare ku? Ku duba, ku gani, ko akwai baƙin ciki irin nawa, Wanda Ubangiji ya ɗora mini, A ranar fushinsa mai zafi.


To, tun daga tsakar rana, duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma.


Da waɗansu na tsaitsayen suka ji haka, suka ce, “Kun ji yana kiran Iliya.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ