Mu kanmu ma dā can mun yi wauta, mun kangare, an ɓad da mu, mun jarabta da muguwar sha'awa da nishaɗi iri iri, mun yi zaman ƙeta da hassada, mun zama abin ƙi, mu kuma mun ƙi waɗansu.
kada mu zama kamar Kayinu, wanda yake na Mugun, har ma ya kashe ɗan'uwansa. To, don me ya kashe shi? Don ayyukansa mugaye ne, na ɗan'uwansa kuwa na kirki ne.