Da manyan firistoci da malaman Attaura suka ji wannan magana suka kuma nemi hanyar hallaka shi, saboda sun tsorata da shi, don duk jama'a na mamaki da koyarwa tasa.
Sauran kwana biyu a yi Idin Ƙetarewa da idin abinci marar yisti, sai manyan firistoci da malaman Attaura suka nemi hanyar kama Yesu da makirci, su kashe shi,
Yesu yana Betanya a gidan Saminu kuturu, yana cin abinci ke nan, sai ga wata mace ta zo da wani ɗan tulu na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tsadar gaske. Sai ta fasa ulun, ta tsiyaye masa man a kā.