Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Markus 13:7 - Littafi Mai Tsarki

7 In kuma kun jin labarin yaƙe-yaƙe da jita-jitarsu, kada hankalinku ya tashi. Lalle ne wannan ya auku, amma ƙarshen tukuna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Sa’ad da kuka ji labarun yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Markus 13:7
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Na bar ku da salama. Salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada ku damu, kada kuma ku ji tsoro.


yana yi musu bayani, yana kuma tabbatarwa, cewa lalle ne, Almasihu yă sha wuya, ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Yesun nan da nake sanar muku, shi ne Almasihu.”


“Kaiton duniya saboda sanadodin tuntuɓe! Lalle sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadin!


Kada zuciyarku ta yi suwu, Kada kuma ku ji tsoro saboda labarin da ake ji a ƙasar, Labari na wannan shekara dabam, na wancan kuma dabam, A kan hargitsin da yake a ƙasar, Mai mulki ya tasar wa mai mulki.


“Kada ka haɗa kanka da jama'a cikin ƙulle-ƙullensu, kada kuma ka ji tsoron abubuwan da su suke jin tsoro.


Ba za ka damu da masifar da za ta auko farat ɗaya ba, irin wadda takan auka wa mugaye kamar hadiri.


Ba ya tsoron jin mugun labari, Bangaskiyarsa tana da ƙarfi, Ga Ubangiji yake dogara.


Ko da rundunar mayaƙa ta kewaye ni, Ba zan ji tsoro ba. Ko da magabtana sun tasar mini, Zan dogara ga Allah.


Dukanmu mutuwa za mu yi, kamar ruwan da ya zube a ƙasa, wanda ba ya kwasuwa, haka za mu zama. Allah ba yakan ɗauke rai kurum ba, amma yakan shirya hanya domin wanda ya shuɗe ba zai ɓata daga gabansa ba.


“Kada ku damu. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni.


Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu ƙwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima.


Mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa su ne ni, har su ɓad da mutane da yawa.


Al'umma za ta tasar wa al'umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a yi ta raurawar ƙasa a wurare dabam dabam, da kuma yunwa. Amma fa duk wannan masomin azaba ne tukuna.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ