Markus 13:11 - Littafi Mai Tsarki11 Sa'ad da suka kai ku gaban shari'a suka miƙa ku, kada ku damu kan abin da za ku faɗa. Amma duk abin da aka yi muku baiwa da shi a lokacin nan, shi za ku faɗa, domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202011 Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |