Ubangiji ya ce, “Ka duba cikin al'umman duniya! Ka gani! Ka yi al'ajabi! Ka yi mamaki! Gama zan yi aiki a kwanakinka, Ko an faɗa maka ba za ka gaskata ba.
Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai, An bayyana shi da jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, Mala'iku sun gan shi, An yi wa al'ummai wa'azinsa, An gaskata da shi a duniya, An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.
Su ne Allah ya so ya sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al'ummai, asirin nan kuwa shi ne Almasihu a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana.
Ba wata maitar da za ta cuci Yakubu, Ba kuwa sihirin da zai cuci Isra'ilawa. Yanzu za a ce, ‘Duba irin abin da Allah ya yi domin Yakubu, wato Isra'ilawa!’
Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, Shi ne ya zama mafificin dutsen gini. Wannan aikin Ubangiji ne, A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.’