Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Markus 12:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sai Yesu ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabin, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Sa’an nan ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ya shuka gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa rami domin matsin inabin, ya kuma gina ɗakin gadi. Sai ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, sa’an nan ya yi tafiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Markus 12:1
38 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kamar mutum ne mai tafiya, in ya bar gida ya wakilta yaransa, kowanne da aikinsa, ya kuma umarci mai jiran ƙofa ya zauna a faɗake.


Sai ya koya musu abubuwa da yawa da misalai. A cikin koyarwa tasa har ya ce musu,


“Kamar mutum ne da zai yi tafiya, ya kira bayinsa, ya danƙa musu dukiyarsa.


Shi ne kuma wanda yake a cikin Ikkilisiyar nan a jeji tare da mala'ikan da ya yi masa magana a Dutsen Sinai, tare da kakanninmu kuma. Shi ne kuma ya karɓo rayayyiyar magana domin ya kawo mana.


Sai ya ce, “Wani mutum mai asali ya tafi wata ƙasa mai nisa neman sarauta yă dawo.


Bayan 'yan kwanaki kaɗan sai ƙaramin ya tattara duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa ƙasa mai nisa. A can ya fallasar da kayansa a wajen masha'a.


Sai ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba.


“To, me kuka gani? An yi wani mutun mai 'ya'ya biyu maza. Ya je wurin na farkon, ya ce, ‘Ɗana, yau je ka ka yi aiki a garkar inabi.’


Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, suna cewa misalai kawai, nake yi.”


Na dasa ka kamar zaɓaɓɓiyar kurangar inabi, zaɓaɓɓen iri mafi kyau. Ta yaya ka lalace haka ka zama rassan kurangar inabi ta jeji, Waɗanda ba zan yarda da su ba?


“A lokacin nan, waɗannan kyawawan gonakin inabi waɗanda suke da kurangar inabi dubu, kuɗin kowace gonar inabi azurfa dubu guda ne, gonakin za su cika da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya.


Suka ce masa, “Ina kake so mu shirya?”


Sai ya gaggaya musu abubuwa da yawa da misalai, ya ce, “Wani mai shuka ya je shuka.


“To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.


Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar.


Sai Yesu ya kira su, ya ba su misali da cewa, “Ina Shaiɗan zai iya fitar da Shaiɗan?


Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Yesu ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izni nake yin abubuwan nan ba.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ