Suka iso Urushalima. Ya shiga Haikalin ya fara korar masu saye da sayarwa daga ciki, ya kuma birkice teburorin 'yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai,
Sai ya yi musu gargaɗi ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira masujadata ɗakin addu'a na dukkan al'ummai’? Amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.”