Markus 11:13 - Littafi Mai Tsarki13 Da ya hango wani itacen ɓaure mai ganye kore shar, sai ya je ya ga ko ya sami 'ya'ya. Da ya isa wurinsa bai ga kome ba sai ganye, don ba lokacin 'ya'yan ɓaure ba ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da ’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin ’ya’yan ɓaure ba ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Isra'ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna, Jama'ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa. Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau, Amma a maimakon haka sai suka zama masu kisankai! Ya zaci za su aikata abin da yake daidai, Amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci!