12 Kashegari da suka tashi daga Betanya, ya ji yunwa.
12 Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa.
Bayan haka, Yesu da ya san duk an gama kome, domin a cika Nassi sai ya ce, “Ina jin ƙishirwa.”
Da ya yi azumi kwana arba'in ba dare ba rana, daga baya yunwa ta kama shi.
Saboda haka, lalle ne yă zama kamar 'yan'uwansa ta kowane hali, domin yă zama Babban Firist, mai jinƙai, mai aminci kuma na al'amarin Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama'a.
har kwana arba'in, Iblis yana gwada shi. A kwanakin nan bai ci kome ba. Da suka ƙare kuwa ya ji yunwa.
Da ya hango wani itacen ɓaure mai ganye kore shar, sai ya je ya ga ko ya sami 'ya'ya. Da ya isa wurinsa bai ga kome ba sai ganye, don ba lokacin 'ya'yan ɓaure ba ne.
Suna wucewa da safe, sai suka ga ɓauren nan ya bushe har saiwarsa.