10 A cikin gida kuma sai almajiransa suka sāke tambayarsa wannan magana.
10 Da suna cikin gida kuma, sai almajiran suka tambayi Yesu game da wannan.
Suka zo Kafarnahum. Da ya shiga gida sai ya tambaye su, “Muhawarar me kuka yi a hanya?”
Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a keɓe suka ce, “Me ya sa mu muka kasa fitar da shi?”
Da suka kaɗaita, masu binsa da su sha biyun nan suka tambaye shi ma'anar misalan.
Abin da Allah fa ya gama, kada mutum ya raba.”
Sai ya ce musu, “Kowa ya saki mata tasa, ya auri wata, zina yake yi da ta biyun.