Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Markus 10:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sai Yesu ya tashi daga nan, ya tafi ƙasar Yahudiya, da kuma hayin Kogin Urdun. Taro kuma ya sāke haɗuwa wurinsa, ya kuma sāke koya musu kamar yadda ya saba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Sai Yesu ya tashi daga nan ya tafi yankin Yahudiya, da kuma ƙetaren Urdun. Taron mutane suka sāke zuwa wurinsa, ya kuma koya musu kamar yadda ya saba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Markus 10:1
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan ya sāke komawa hayin Kogin Urdun, wurin da Yahaya ya fara yin baftisma, ya zauna a can,


Sai ya koya musu abubuwa da yawa da misalai. A cikin koyarwa tasa har ya ce musu,


Bayan haka ya ce wa almajiran, “Mu koma ƙasar Yahudiya.”


Da saukar Yesu sai ya ga taro mai yawa, ya kuma ji tausayinsu, domin kamar tumaki suke ba makiyayi. Ya fara koya musu abubuwa da yawa.


Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane.


Sun juya mini baya, ba su fuskance ni ba, ko da yake na yi ta koya musu, amma ba su saurara ga koyarwata ba.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a bayyane, na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban faɗi kome a ɓoye ba.


Ya yi mamakin rashin bangaskiyarsu. Sai ya zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.


Yesu ya sāke fita bakin teku. Duk jama'a suka yi ta zuwa wurinsa, yana koya musu.


Saboda hikimar Mai Hadishi ya koya wa mutane ilimi. Ya auna, ya bincika, ya tsara karin magana da lura sosai.


Nan take Yesu ya ce wa taron jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi? Kowace rana nakan zauna a Haikali ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba.


Suka shiga Kafarnahum. Ran Asabar kuwa, ya shiga majami'a yana koyarwa.


Da Asabar ta yi, sai ya fara koyarwa a majami'a. Mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki, suna cewa, “Ina mutumin nan ya sami wannan abu duka? Wace hikima ce aka ba shi haka? Dubi irin waɗannan mu'ujizan da ake aikatawa ta hannunsa!


Sai waɗansu Farisiyawa suka zo wajensa don su gwada shi, suka tambaye shi suka ce, “Halal ne mutum ya saki mata tasa?”


Sa'ad da Yesu yake koyarwa a Haikalin sai ya ce, “Ƙaƙa malaman Attaura za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne?


Kowace rana ina tare da ku a Haikalin ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba. Amma an yi haka ne fa domin a cika Littattafai.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ