“Bayan wannan zan zubo Ruhuna a kan jama'a duka, 'Ya'yanku mata da maza za su iyar da saƙona, Tsofaffinku kuwa za su yi mafarkai, Samarinku za su ga wahayi da yawa.
“ ‘Allah ya ce, A zamanin karshe zai zamanto zan zubo wa dukan 'yan adam Ruhuna. 'Ya'yanku mata da maza za su yi annabci, Wahayi zai zo wa samarinku, Dattawanku kuma za su yi mafarkai.
“Ni dai, da ruwa nake muku baftisma, shaidar tubarku, amma mai zuwa bayana, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.
“Zan ba da ruwa ga ƙasa mai ƙishi, In kuma sa rafuffuka su yi gudu a hamada. Zan kwararo da albarka a kan 'ya'yanku, In sa albarkata kuma a kan zuriyarku.
sai Yahaya ya amsa wa dukansu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake yi muku baftisma, amma wani yana zuwa wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa in ɓalle ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.
Dā kam, ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma kasance a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’