Bayan aljanin nan ya yi ihu, sai ya buge shi da gaske, jikinsa na rawa, ya rabu da shi. Yaron kuma ya zama kamar matacce, har ma yawancin mutane suka ce, “Ai, ya mutu!”
Ga shi, aljani yakan hau shi, yakan yi ihu ba zato ba tsammani. Aljanin yakan buge shi, jikinsa yana rawa, har bakinsa yana kumfa. Ba ya barinsa sai ya kukkuje shi ƙwarai.
Duk suka yi mamaki, har suka tanttambayi juna suna cewa, “Kai, mene ne haka? Tabɗi! Yau ga baƙuwar koyarwa! Har baƙaƙen aljannu ma yake yi wa umarni gabagaɗi, suna kuwa yi masa biyayya!”