Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Markus 1:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Nan da nan da ya kira su, suka bar ubansu Zabadi a cikin jirgin tare da ma'aikata, suka bi shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Ba da ɓata lokaci ba, ya kira su, sai suka bar mahaifinsu Zebedi a cikin jirgin ruwan, tare da ’yan haya, suka kuwa bi shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Markus 1:20
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Duk mai zuwa wurina, in bai fi ƙaunata da ubansa, da uwa tasa, da mata tasa, da 'ya'yansa, da 'yan'uwansa mata da maza, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba.


Yesu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko 'yan'uwansa mata, ko 'yan'uwansa maza, ko uwa tasa, ko ubansa, ko 'ya'yansa, ko gonakinsa, sabili da ni da kuma bishara,


Wanda duk ya fi son ubansa ko uwarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba.


Saboda haka, a nan gaba ba mā ƙara duban kowane mutum bisa ga ɗabi'ar jiki kawai, domin ko da yake mun taɓa duban Almasihu bisa ga ɗabi'ar jiki, yanzu ba ma ƙara dubansa haka.


Sai ya bar shanun noma, ya sheƙa gun Iliya, ya ce, “Bari in sumbaci mahaifina da mahaifiyata, in yi bankwana da su, sa'an nan in zo in bi ka.” Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Koma, me na yi maka?”


Wanda ya ce wa mahaifinsa da mahaifiyarsa, ‘Ban kula da ku ba.’ Ya ce wa 'yan'uwansa su ba nasa ba ne. Ya kuma ƙyale 'ya'yansa, Domin sun kiyaye maganarka, Sun riƙe alkawarinka.


Da ya ci gaba kaɗan, sai ya ga Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirginsu suna gyaran taruna.


Suka shiga Kafarnahum. Ran Asabar kuwa, ya shiga majami'a yana koyarwa.


Da suka kawo jiragensu gaci, suka bar kome duka suka bi shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ