Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Markus 1:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Da ya ci gaba kaɗan, sai ya ga Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirginsu suna gyaran taruna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Da ya yi gaba kaɗan, sai ya ga Yaƙub ɗan Zebedi, da ɗan’uwansa Yohanna a cikin jirgin ruwa, suna gyaran abin kamun kifinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Markus 1:19
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

har ma ya sare Yakubu ɗan'uwan Yahaya da takobi.


Da suka shiga birnin, suka hau soro inda suke zama, wato Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da Andarawas, da Filibus, da Toma, da Bartalamawas, da Matiyu, da Yakubu na Halfa, da Saminu Zaloti, da kuma Yahuza na Yakubu.


Sai ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kuma fara jin wahala gaya, yana damuwa ƙwarai.


Yakubu da Yahaya, 'ya'yan Zabadi, suka kusato shi, suka ce masa, “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙe ka.”


Bayan kwana shida Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. Sai kamanninsa ya sāke a gabansu,


Bai bar kowa ya bi shi ba sai Bitrus, da Yakubu, da kuma Yahaya ɗan'uwan Yakubu.


da Yakubu ɗan Zabadi, da kuma ɗan'uwansa Yahaya, ya sa musu suna Buwanarjis, wato 'ya'yan tsawa.


Da ya ci gaba sai ya ga waɗansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da ubansu Zabadi, suna gyaran tarunansu. Sai ya kira su.


Nan da nan kuwa suka watsar da tarunansu, suka bi shi.


Nan da nan da ya kira su, suka bar ubansu Zabadi a cikin jirgin tare da ma'aikata, suka bi shi.


Bitrus, da Toma wanda ake kira Ɗan Tagwai, da Nata'ala na Kana ta ƙasar Galili, da 'ya'yan nan na Zabadi, da kuma waɗansu almajiransa biyu, duk suna nan tare,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ