Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Markus 1:14 - Littafi Mai Tsarki

14 To, bayan an tsare Yahaya, sai Yesu ya shigo ƙasar Galili, yana yin bisharar Allah,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Bayan da aka sa Yohanna a kurkuku, sai Yesu ya shigo cikin Galili, yana shelar bisharar Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Markus 1:14
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane.


To, da Yesu ya ji an tsare Yahaya, sai ya tashi zuwa ƙasar Galili.


Ya kuwa zo ya yi muku albishirin salama, ku da kuke nesa, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa.


Ba da daɗewa ba Yesu ya zazzaga birni da ƙauye yana wa'azi, yana yin bisharar Mulkin Allah. Sha biyun nan kuwa suna tare da shi,


Da suka sa masa rana, sai suka zo masaukinsa, su da yawa. Sa'an nan ya yi ta yi musu bayani, yana ta shaidar musu Mulkin Allah, tun daga safe har magariba, yana ƙoƙarin rinjayarsu a kan Yesu, ta hanyar Attaurar Musa da littattafan annabawa.


Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.


To, ga shi, yanzu na san dukanku ba za ku ƙara ganina ba, ku da na zazzaga cikinku ina yi muku bisharar Mulkin Allah.


Sai ya ce wa barorinsa, “Wannan, ai, Yahaya Maibaftisma ne, shi aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”


To, da Yahaya ya ji a kurkuku labarin ayyukan Almasihu, sai ya aiki almajiransa,


Tun daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin Mulkin Sama ya kusato.”


Daga Bulus, bawan Yesu Almasihu, manzo kirayayye, keɓaɓɓe domin yin bisharar Allah,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ