Yana magana ke nan sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.”
Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.
Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.
“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.
Mala'ikan ya amsa mata ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, Ikon Maɗaukaki kuma zai lulluɓe ki. Saboda haka Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.
tun daga baftismar da Yahaya ya yi, har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi daga wurinmu aka kai shi zuwa Sama, wato ɗaya daga cikin mutanen nan ya zama shaidar tashinsa daga matattu, tare da mu.”