Malaki 3:16 - Littafi Mai Tsarki16 Sa'an nan mutane waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da junansu, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya ji abin da suke cewa. A gabansa aka rubuta a littafin tarihin waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuwa girmama shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202016 Sa’an nan waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da juna, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya kuma ji. A gabansa aka rubuta a littafin tarihi waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuma girmama sunansa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”