Malaki 2:14 - Littafi Mai Tsarki14 Kuna tambaya cewa, “Me ya sa ba ya karɓar hadayunmu?” Ai, domin ya sani ka keta alkawarin da ka yi wa matarka ta ƙuruciya ne, wadda ka ci amanarta ko da yake ita abokiyar zamanka ce, da matarka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Kukan ce, “Don me ba ya karɓan hadayunmu?” Ai, domin Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matar ƙuruciyarka, gama ka keta amanar da ka yi mata, ko da yake ita abokiyar zamanka ce, matar aurenka ta alkawari. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”