Malaki 2:12 - Littafi Mai Tsarki12 Ubangiji zai lalatar da dukan wanda ya aikata wannan, wato wanda ya farka da wanda ya amsa, ko wanda yake kawo hadayu ga Ubangiji Mai Runduna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Game da mutumin da ya aikata wannan, ko wane ne shi, bari Ubangiji yă yanke shi daga tentunan Yaƙub, ko da ma ya kawo hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu'a ga gumaka. Suna jin daɗin al'amuran banƙyama a lokacin yin sujada.