Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Malaki 2:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Mutanen Yahuza sun keta alkawarin da yake tsakaninsu da Allah, sun aikata mugun abu a Isra'ila, da a Urushalima. Gama sun ƙazantar da Haikalin da Ubangiji yake ƙauna, sun kuma auro matan da suke bauta wa gumaka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Yahuda ya ci amana. An yi abin kunya a Isra’ila da kuma a Urushalima. Yahuda ya ƙazantar da wuri mai tsarkin da Ubangiji yake ƙauna, ta wurin auren ’yar wani baƙon allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Malaki 2:11
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma matsorata, da marasa riƙon amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibiritu, wanda yake shi ne mutuwa ta biyu.”


“Amma sun ta da alkawarina kamar Adamu, Sun ci amanata.


Wani yakan yi lalata da matar maƙwabcinsa, wani kuma ya kwana da matar ɗansa, wani ya kwana da 'yar'uwarsa, wato 'yar mahaifinsa.


yana ba da bashi da ruwa da ƙari, wannan ba zai rayu ba, gama ya aikata dukan abubuwan nan masu banƙyama. Zai mutu lalle, alhakin jininsa kuwa yana a kansa.


Sa'an nan za ku zo ku tsaya a gabana a wannan Haikali, wanda ake kira da sunana, ku ce, “An cece mu,” don kawai ku ci gaba da yin dukan waɗannan abubuwan banƙyama?


Isra'ila tsattsarka ce ta Ubangiji, Nunar fari ta girbina. Dukan waɗanda suka ci daga cikinki sun yi laifi, Masifa za ta auko miki. Ni Ubangiji, na faɗa.”


Sai jama'ar Allah suka taru suka shiga yi wa Ba'al sujada, a Feyor, Suka ci hadayun da aka miƙa wa matattun alloli.


Sai Shekaniya ɗan Yehiyel, daga zuriyar Elam, ya yi wa Ezra magana, ya ce, “Mun yi wa Allahnmu rashin aminci, gama mun auri mata baƙi daga mutanen ƙasar, amma duk da haka akwai sauran bege ga Isra'ila.


Domin haka kada ku aurar musu da 'ya'yanku mata, kada kuma ku auro wa 'ya'yanku 'yan matansu, kada kuma ku nemi zaman arziki da su. Idan kun yi biyayya za ku yi ƙarfi, ku ci albarkar ƙasar, har ku bar ta gādo ga 'ya'yanku har abada.’


Suka yi aurayya da su, suka kuma yi sujada ga gumakansu.


Gama ku keɓaɓɓun mutane ne na Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku kuwa ya zaɓo ku daga cikin dukan al'umman duniya ku zama mutanensa, wato abin gādonsa.”


Sai ku zama tsarkakakku a gare ni, gama ni Ubangiji Mai Tsarki ne, na kuwa keɓe ku daga sauran al'umman duniya don ku zama nawa.


Wannan shi ne jawabin da Ubangiji ya ba Malakai ya faɗa wa jama'ar Isra'ila.


Duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza ba ta juyo wurina da zuciya ɗaya ba, sai a munafunce, ni Ubangiji na faɗa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ