Ubangiji Mai Runduna ya ce wa firistoci, “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bara kuwa yakan girmama maigidansa. Ni Ubanku ne, me ya sa ba ku girmama ni ba? Ni kuma Maigidanku ne, me ya sa ba ku ganin darajata? Kun raina ni, duk da haka kuna tambaya cewa, ‘Ƙaƙa muka raina ka?’
“Ku ji wannan, ya ku firistoci! Ku saurara, ya mutanen Isra'ila! Ku kasa kunne, ya gidan sarki! Gama za a yi muku hukunci, Domin kun zama tarko a Mizfa, Da ragar da aka shimfiɗa a bisa Tabor.
Sa'an nan za ka faɗa musu, Ubangiji ya ce, ‘Ga shi, zan sa dukan mazaunan ƙasar su bugu da ruwan inabi, wato sarakunan da suka hau gadon sarautar Dawuda, da firistoci, da annabawa, da dukan mazaunan Urushalima.
La'ananne ne macucin da yake da lafiyayyun dabbobi da ya alkawarta zai ba ni daga cikin garkensa ya kuwa miƙa mini hadaya ta haramtacciyar dabba. Gama ni babban Sarki ne, dukan al'ummai kuwa suna jin tsoron sunana, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la'ana, zan la'antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la'antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.