Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Malaki 1:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Yadda kuka yi ke nan. Kun miƙa haramtacciyar hadaya ta abinci a kan bagadena, sa'an nan kuna cewa, ‘Ta ƙaƙa muka raina ka?’ To, zan faɗa muku, don kun ƙazantar da bagadena.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 “Kun ajiye abinci mai ƙazanta a kan bagadena. “Sai kuka ce, ‘Yaya muka ƙazantar da kai?’ “Ta wurin cewa teburin Ubangiji abin reni ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Malaki 1:7
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Amma ku kun raina ni da yake kuka ce bagadena ba kome ba ne, kuna raina abincin da kuke ajiyewa a kai.


Ba dama ku sha a ƙoƙon Ubangiji, ku kuma sha a na aljannu. Ba dama ku ci abinci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a na aljannu.


Sa'ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, kuna tsammani wannan daidai ne? Ko kuwa sa'ad da kuka kawo gurguwar dabba ko marar lafiya wannan daidai ne? Ku ba mai mulkinku irin wannan ku gani. Zai yi murna? Ko za ku sami tagomashi, a wurinsa? Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”


Idan yana da wani lahani kamar gurguntaka ko makanta, ko kowane irin mugun lahani, to, kada ku miƙa shi hadaya ga Ubangiji Allahnku.


Sai su kasance da tsarki, kada su ƙasƙantar da sunana domin su ne masu kawo hadaya ta ci, masu ƙone hadayu da wuta gare ni, don haka sai su kasance da tsarki.


A kowace hadaya ta gari da za a kawo wa Ubangiji, ba za a sa yisti ba, gama ba za a yi hadayar ƙonawa ga Ubangiji da yisti, ko da zuma ba.


Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone da wuta ga Ubangiji.


Dole jama'a su gan su da tsarki, gama suna miƙa hadaya ta ci gare ni. Ni ne Ubangiji, ni mai tsarki ne, na kuwa tsarkake mutanena.


Za su shiga Wuri Mai Tsarki, su kusaci teburina, su yi mini hidima, su kuma kiyaye umarnina.


Kuka kuma ce, ‘Mun gaji da wannan irin abu fa!’ Kuna hura mini hanci. Kukan kawo satacciyar dabba, ko gurguwa ko marar lafiya, ku yi mini hadaya da ita! Kuna tsammani zan karɓi wannan daga gare ku?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ