Malaki 1:6 - Littafi Mai Tsarki6 Ubangiji Mai Runduna ya ce wa firistoci, “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bara kuwa yakan girmama maigidansa. Ni Ubanku ne, me ya sa ba ku girmama ni ba? Ni kuma Maigidanku ne, me ya sa ba ku ganin darajata? Kun raina ni, duk da haka kuna tambaya cewa, ‘Ƙaƙa muka raina ka?’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bawa kuma yakan girmama maigidansa. In ni mahaifi ne, ina girman da ya dace da ni? In ni maigida ne, ina girman da ya dace da ni?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Ku firistoci, ku ne kuka rena sunana. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka rena sunanka?’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”